in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci a fara shirin shiga sabuwar gwamnati a Sudan ta Kudu
2014-12-15 15:56:10 cri

Magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Lahadin nan ya bukaci jam'iyyun siyasa a kasar Sudan ta Kudu da su fara shirin kafa sabuwar gwamnati domin a samo shawo kan matsalar da ake fuskanta sama da shekara daya da ta wuce.

Ban Ki-moon, ta bakin kakakinsa ya yi nuni da cewa, wannan ranar ta cika shekara daya cif da tashin hankali ya barke a kasar ta Sudan ta Kudu wadda ita ce karamar kasa a duniya a yanzu, yana mai nuna damuwarsa yadda dukkan bangarori suka kasa cimma wata yarjejeniya ta zaman lafiya. Ya ce, shugabannin sun bar son zuciya ya lalata makomar kasar baki daya.

Shugaban na MDD ya yi kira ga shugabannin bangarorin biyu duka da su amince da fara shirin shiga sabuwar gwamnati wanda zai tafi da kowa tare da raba ikon daidai wa daida, ya kuma shawo kan dukkan matsalar da ta kawo sabani a yanzu, sannan ya tabbatar kowa ya dauki nauyin laifuffukan da ya aikata cikin shekara dayan da ta gabata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China