Rundunar sojin Najeriya ta ce, dakarunta sun samu nasarar fatattakar mayakan kungiyar Boko Haram daga garin Madagali, wanda shi ne gari na karshe da 'yan tada-kayar bayan ke rike da shi a jihar Adamawa.
Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade, ya ce, nasarar da sojojin suka samu ta biyo bayan dauki ba dadin da suka kwashe tsahon lokaci suna kwabzawa da 'yan Boko Haram. Kaza lika sanarwar ta ce, ba a samu asarar rayuka daga bangaren sojojin Najeriyar ba.
Olukolade ya kara da cewa, yanzu haka sojojin na can na daukar matakan tabbatar da kare garin, tare da dawo da yanayin tsaro.
A wani batun mai alaka da wannan kuma, kakakin ofishin yakin neman zaben dan takarar shuagabancin Najeriya karkashin jam'iyyar APC Garba Shehu, ya jinjinawa kwazon sojojin Najeriya, game da kakkabe yankunan arewa maso gabashin kasar daga ayyukan kungiyar Boko Haram.
Sai dai a daya hannun, Shehu ya bayyana mamakinsa, ga yadda gwamnatin kasar ta kyale kungiyar har ta yi karfin gaske kafin daukar irin wannan mataki na dakile ta, ya ce, hakan ya baiwa 'ya'yan kungiyar damar kisan dubban fararen hula, tare da jefa yankin na arewa maso gabashin Najeriya cikin wani mawuyacin hali. (Saminu)