Hukumar zabe mai zaman kan ta a Najeriya, ta jaddada aniyar gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci.
Shugaban kwamitin hukumar ta INEC mai lura da harkokin wayar da kan jama'a da raba katunan zabe na din din din Dr. Chris Iyimoga, shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, INEC za ta tabbatar da nasarar zabukan kasar na karshen watan nan, da kuma na watan Afirilun dake tafe.
Dr. Iyimoga ya kara da cewa, tun lokacin da aka dage zaben kasar daga watan Fabarairun da ya shude, ma'aikatan hukumar ba su huta ba, inda suka ci gaba da daukar karin matakan inganta tsarin zaben.
A cewarsa, kawo yanzu IVEC ta raba katunan zaben na din din din da yawan su ya kai kaso 80.24 bisa dari. (Saminu)