in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama wasu mata 'yan kunar bakin wake biyu a Chadi
2015-02-04 10:44:29 cri

Wasu mata biyu dauke da gurmeti da wasu nakiyoyi masu fashewa, sun shiga hannun jami'an tsaro a ranar Litinin a Toubia, wani yankin kasar Chadi dake kusa da birnin N'Djamena, bayan sun ratso kasar Kamaru a yayin da suka fito daga Najeriya a jajibirin karbe garin Gambaru da sojojin Najeriya suka yi daga hannun Boko Haram tare da taimakon sojojin kasar Chadi, a wani labarin da Xinhua ya samu daga wata mijiyar tsaro a ranar Talata da safe.

Matan biyu suna da niyyar tada nakiyoyin nasu a N'Djamena, babban birnin kasar Chadi. Matan dai na dauke da wadannan nakiyoyin da aka sanya cikin bududuwan da ake yanke, sannan aka rufe wayar karfe, domin a yi tsammanin suna dauke da madara, in ji wannan majiya ta wayar tarho. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China