Gwamnatin tarayyar Nigeriya ta bukaci al'ummarta da su kasance kan shirin ko da yaushe sakamakon sauyin dabara da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi na amfani da 'yan kunar bakin wake a ci gaba da suke na bata wa kasar suna.
Wannan gargadin tsaron ya zo ne bayan wani bincike da sojojin kasar tare da hadin gwiwwar na sauran kasashe makwabta a karkashin shirin sojin hadin gwiwwar kasashe daban daban daga dukkan sansanoninsu, inda suka bukaci 'yan Nigeriya da kada su yi sake, su kuma sa ido a kan duk wassu masu yanayi da 'yan kunar bakin waken da aka riga aka sauya masu tunani ko kuma kungiyar ta shayar da su kwayoyin fitar hankali.
Sanarwar da aka fitar wa manema labaran Xinhua na bayyana cewa, Marilyn Ogar, kakakin hukumar leken asirin kasar ta yi kira ga 'yan Nigeriya da su kasance cikin shiri ko da yaushe, suna lura da wuraren da ke da cunkosun mutane.
Marilyn Ogar ta ce, a bayyane ake cewa, sakamakon nasarar da aka samu ta samamen da aka kai wa kungiyar ta sama da kuma matsin da sojoji suka yi wa 'yan ta'addan a arewa maso gabashi wanda ya rage karfin kungiyar, mambobinta yanzu sun tarwatse, don haka sun nemi wassu hanyoyi na huce haushin su a kan al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba.
Ta ce, masu zirga zirga su guji shiga motocin da ba su da rajista a bakin hanya, su tabbatar sun shiga tashar mota domin bin motocin da aka ma rajista a wajen manajojin tasha domin a bincike fasinjoji da kayayyakinsu lokacin da za su shiga tashar, sannan kuma ta ce, su rika duba sabbin fuskokin da ba su saba gani ba a kewayensu da za su zama direbobi da masu sayar da tikitin shiga mota. (Fatimah)