Dakarun kungiyar tarayyar Afirka da ke kasar Somalia (AMISON) ta bayyana cewa, mayakanta da na sojojin gwamnatin Somalia sun kaddamar da hare-hare kan maboyar mayakan Al-Shabaab da ke kudancin kasar Somalia.
AMISON ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, dakarun kawancen sun yi nasarar kwace muhimmin garin nan na Bulo Marer da ke yankin Lower Shabelle daga hannun mayakan na Al-Shabaab.
Sai dai babu wani karin haske game da wadanda suka jikkata a arangamar ta baya-bayan nan da ta wakana tsakanin mayakan na Al-Shabaab da kuma dakarun na AU da sojojin gwamnatin na Somalia ba.
Haka za lika su ma mayakan na Al-Shabaab ba su ce komai ba game da kwace garin na Bulo Marer da sauran garuruwa da ke kudancin Somalia daga hannunsu, wadanda suka kasance karkashin ikonsu na tsawon sama da shekaru da dama.
Mai rikon mukamin shugabar tawagar ta AMISON Lydia Wanyoto Mutende ta ce, a baya-bayan nan sojojin gwamnatin Somalia da dakarun AU suna samun galaba a kan mayakan na Al-Shabaab, matakin da ta ce wata babbar nasara ce kan fafatawar da ake yi da mayakan na Al-Shabaab. (Ibrahim)