Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta bullo da wani shiri bisa matakai biyar dake cikin tsarin kokarinta domin takaita haduran karancin wutar lantarki a tsawon shekaru uku masu zuwa, in ji ma'aikatar makamashin kasar a ranar Litinin.
Wannan dabara ta zo domin magance matsalar katsewar wutar lantarki dake shafar Afrika ta Kudu a shekarun biyu na baya bayan nan dalilin yadda aka takaita samar da wutar lantarki sosai. Ana samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 14,000 da kuma kashi daya bisa uku da kamfanin Eskom ke samarwa, ba'a amfani da shi a yanzu haka. Fiye da megawatt 8000 na wadannan megawatt 14,000 na karancin samar da wutar lantarki, yana da nasaba da ayyukan gyarawa ba zata.
Sabon shirin da gwamntin kasar ta amince da shi a makon da ya gabata ya hada matakan gaggawa da ya kamata Eskom ya dauka a cikin kwanaki talatin masu zuwa, in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa. Kamar yadda shirin ya bayyana, za'a isar iskan gas domin sarrafa daga megawatt 500 zuwa megawatt 2000 a tsawon gajeren lokaci zuwa dogon lokaci. (Maman Ada)