Kasashen Gambiya, Senegal, Guinea da Guinea-Bissau za su ci gajiyar wani shirin samar da tashar wutar lantarki mai sauki domin kawo karshen matsalar wutar lantarki da suke fuskanta, in ji Jutino Viera, sakatare janar na kungiyar aiwatar da amfanin kogin Gambiya (OMVG), a ranar Talata a birnin Banjul, hedkwatar kasar Gambiya.
Samun wutar lantarki cikin sauki, zai kyautata wajen bunkasa tattalin arzikin shiyyar da kuma bunkasa dunkulewar wannan shiyya. Karin wutar lantarki da wannan shirin ke bayarwa zai taimaka wajen kara tsaron makamashin shiyyar, in ji mista Viera. Kungiyar OMVG ta fara aikin kafa tashoshin wutar lantarki biyu a kasar Guinee masu karfin Megawatt 386, in ji mista Viera a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata. (Maman Ada)