in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sa ido na ECOWAS sun isa Najeriya
2015-03-06 09:53:38 cri

Rukunin farko na jami'an sa ido ga babban zaben Najeriya daga kungiyar ECOWAS sun isa kasar, gabanin zaben shugaban kasa a ran 28 ga watan Maris din nan, da kuma na gwamnoni da za a yi a ranar 11 ga watan Afirilu.

Tawagar jami'an wadda ke kunshe da wani kaso na wakilai 250, da ake fatan za su wakilci kungiyar ta ECOWAS, na karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Ghana John Kuffour. Ana kuma sa ran ragowar wakilan kungiyar su 18 za su isa Najeriyar cikin mako mai zuwa.

A cikin watan Janairun da ya shude ne dai aka raba jami'an tawagar zuwa 5 cikin yankunan kasar 6, kafin dage zabukan kasar, lamarin da ya sanya su komawa gida domin jiran sabon lokacin da aka sanya.

Kaza lika shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Kadre Ouedraogo, ya jagoranci wasu wakilan kungiyar, domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da siyasar Najeriya, biyawa bayan dage lokacin zaben.

Tura jami'an sa ido ga zabukan kasashen Afirka dai mataki ne, wanda ya dace da manufar kungiyar ta ECOWAS, game da bunkasa tsarin dimokaradiyya da shugabanci na gari.

An dai dage zaben Najeriya ne bayan da hukumomin tsaron kasar suka ce ba za su iya ba da tabbancin tsaron al'umma a lokacin zaben ba, sakamakon kalubalen tsaro, musamman a arewa maso gabashin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China