Kwararrun kiwon lafiya na kasar Sin wadanda aka tura Afrika ta yamma sun horas da ma'aikatan kiwon lafiya na Afrika ta yamma kimanin 10,202 a game da yadda za'a kula da majiyyata da suka kamu da cutar Ebola mai saurin kashe jama'a.
Wata jarida wacce ke da alaka da hukumar lafiya da tsarin iyali ta kasar Sin ita ce ta ba da rahoton kokarin da kwararrun kiwon lafiya na kasar Sin ke yi a Afrika ta yamma.
Tun dai a watan Nuwambar shekarar 2014 ne kasar Sin ta tura da wata tawagar kwararrun likitoci da ma'aikatan lafiya guda 64 zuwa Afrika ta yamma domin ba da guddumuwa wajen yaki da cutar Ebola.
Kawo ya zuwa yanzu kwararrrun sun horas da likitoci 5,093 da kuma masu aikin nas da ma'aikatan kiwon lafiya daga Saliyo. Hakazalika sun horas da wasu ma'aikatan 1,823 daga Liberia, sai kuma wasu adadin ma'aikatan kiwon lafiya 1,481 daga Guinea. Akwai kuma adadin ma'aikatan kiwon lafiya 1,805 wadanda suka fito daga kasashe shida dake yankin Afrika ta yamma.
Jaridar ta ce, wannan ita ce tawaga ta farko daga kasar Sin wadda ta gudanar da horo ga ma'aikatan kiwon lafiya na kasashen Afrika ta yamma, hakan ya baiwa China damar gabatar da kwarewarta a wajen kula da masu fama da cutar Ebola, musamman saboda a can baya kasar Sin ta samu nasarar dakile bazuwar cutar SARS.
Tun bayan barkewar cutar Ebola a Afrika ta yamma, kasar Sin ta kasance tana bayar da agajin kayayyakin aiki na kiwon lafiya da kuma kwararrun wadanda za su taimaka wajen dakile cutar ta Ebola. (Suwaiba)