in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Cote d'Ivoire ya yi alkawarin yaki da kungiyoyi masu dauke da makamai
2015-03-06 10:51:36 cri

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya yi alkawari a ranar Alhamis a Soubre dake kudu maso yammacin kasar wajen yaki ba kakkautawa da kungiyoyin masu fashi da makami kan hanyoyin kasar.

A cewar Ouattara dake ziyarar aiki a wannan yanki, gwamnati za ta kara rubanya kokarinta domin ganin an magance matsalolin rashin tsaro da wasu mutane dauke da makamai da ake kira "masu fashi da makami kan hanya".

A nasa ra'ayi, ganin yadda yankin kudu maso yammacin kasar ke kunshe da arzikin noman Cacao, ya sa yankin ke fuskantar hare haren 'yan fashi da makami jeri-jeri.

Sojoji da jandarma sun tura kayayyakin aiki sosai, kuma za mu ci gaba da tallafa musu. Za mu ci gaba da farautar wadannan mutane, kuma za mu samu nasarar kawar da su, in ji shugaba Ouattara.

A lokaci da dama dai, manyan jami'an kasar Cote d'Ivoire sun sha bayyana niyyarsu ta kawar da wannan annoba ta kungiyoyin masu fashi da makami dake gurbata zaman lafiyar al'ummomi a kan hanyoyin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China