in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a Mali
2015-03-09 10:08:43 cri

A jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya yi allah wadai da kakkausar murya kan harin ta'addancin da aka kai sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da ke Mali, inda ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Mali da ta gudanar da bincike don ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Wata sanarwa da kwamitin mai mambobi 15 ya fitar, ta bayyana cewa, harin da aka kai kan sansanin dakarun na MINUSMA da ke garin Kidal ya yi sanadiyar mutuwar yara biyu da kuma sojan kasar Chadi daya baya ga wasu da dama da suka jikkata.

Shi ma da ya ke jawabi, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi allah wadai da wannan hari, inda ya mika sakon ta'aziya ga gwamnatin Mali da kuma iyalan wadanda harin ya rutsa da su, sannan ya bukaci gwamnatin Mali da ta hanzata gudanar da bincike don ganin an gurfanar da wadanda suka aikata harin a gaban kuliya.

Mambobin kwamitin sun bayyana cewa, ayyukan ta'addanci na kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, don haka akwai bukatar daukar matakan da suka dace bisa tsarin dokokin MDD, don ganin an kawar da ayyukan ta'addanci a duniya.

Bugu da kari, mambobin kwamitin sulhun sun nanata kudurinsu na baiwa wakilin musamman na sakatare janar da ke Mali, Mongi Hamdi da tawagar MINUSMA, ta yadda za a taimakawa al'ummar Mali da hukumomin kasar a kokarin da suke na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kasar Mali dai ta fada cikin tashin hankali ne a shekarar 2012, tun bayan juyin mulkin sojan da aka yi a kasar. Kuma yanzu haka kasar Faransa na da dakaru sama da 3,000 a yammacin Afirka a yakin da ake da masu tayar da kayar baya, baya ga dakarun MINUSMA sama da 8,000 da kwamitin sulhu ya amince a tura cikin watan Afrilun shekarar 2013. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China