in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya yaba da ci gaban tattalin arzikin Mozambique
2014-05-13 10:38:28 cri

Bankin ba da lamuni na IMF ya jinjinawa kokarin da mahukuntan kasar Mozambique suka yi, wajen bunkasa tattalin arziki, da rage hauhawar farashi a kasar. Ko da yake a hannu guda, bankin na IMF ya bukaci da aka kara azama wajen samar da ayyukan yi, domin bunkasa kanana da matsakaitan masana'antun kasar.

Wani rahoton kamfanin dillancin labarun kasar ta Mozambique AIM, ya hakaito hukumar gudanarwar IMF din na cewa, an riga an kammala nazarin ci gaban da tattalin arzikin kasar ya samu a karo na biyu, karkashin shirin tallafi na PSI da bankin ba da lamunin ke daukar nauyi.

Da yake tsokaci game da muhimman sassa masu alaka da kalubalen da har yanzu kasar ta Mozambique ke fuskanta, mataimakin darekta a bankin na IMF Naoyuki Shinohara, ya ce, akwai matukar bukatar aiwatar da manufofin gwamnati yadda ya kamata, domin kaucewa karuwar gibin da aka fuskanta a bara.

Har ila yau Mr. Shinohara ya bayyana inganta kwarewa a fagen gudanar da ayyukan hukuma, a matsayin hanyar tabbatar da dorewar cin gajiya da kasar ke samu daga bunkasar tattalin arzikin ta.

Bugu da kari jami'in na IMF ya ce, karbar bashi daya ne daga hanyoyin cimma burin samar da ababen more rayuwa, muddin dai an yi amfani da damar ta hanyar da ta dace. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China