Wata babbar wakiliyar MDD a kasar Cote d'Ivoire Aichatou Mindaoudou ta ce, za'a ci gaba da rage sojojin kiyaye zaman lafiya a Cote d'Ivoire, to amma kuma dole ne a inganta zafin naman sauran dakarun da za'a bari a kasar domin a shirya su yadda za su iya tabbatar da tsaro a kasar a lokacin zaben shekarar 2015.
A cikin jawabin da ta yi, Mindaoudou ta ce, kasar Cote d'Ivoire na kan hanyar samun zaman lafiya mai dorewa, a inda ta bayyana kokarin da ake yi na tabbatar da an samu hadin kan kasa.
Wakiliyar MDD ta bayyana wani ci gaban da aka samu na tattalin arziki a kasar, da kuma wani sabon kokari da ake yi na samun daidaito da juna, duk kuwa da yake ta ce, akwai kalubale a fuskar tsaro, musamman da yake an kusa gudanar da zaben da aka tsara gudanarwa a kasar.
Ta kara da cewar, har yanzu akwai matsaloli a tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da 'yan adawa na siyasa, kana kuma ga matsalar aikata laifuka a gefe guda, da sauran barazana ta tsaro dake addabar kasar dake Afrika ta yamma. (Suwaiba)