Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Mali MINUSMA, ta bayyana matukar takaici game da harin da aka kaiwa sansanin ta dake arewacin Mali.
Da ya ke bayyana bakin cikin faruwar wannan lamari, babban jami'in tawagar ta MINUSMA David Gressly, ya ce, an harba rokoki 9 kan sansanin dake Tessalit, ko da yake bai fayyace yawan wadanda harin ya ritsa da su ba.
Gressly ya ce, ya zama wajibi, a gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kuliya. Kana MDD ba za ta gajiya ba, wajen daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin tabbatar da zaman lafiya da samar da daidaito a Mali.
Sansanin da aka kaiwa hari dai na kunshe ne da jami'an tawagar MINUSMA, da dakarun sojin kasar Mali, da kuma sojojin Faransa dake tallafawa yakin da ake yi da 'yan tawayen kasar.
Tun cikin watan Maris na shekarar 2012 kawo wannan lokaci, yankin arewacin Mali ke ci gaba da kasancewa matattarar mayakan 'yan tawayen kasar Mali. (Saminu)