Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Alhamis din nan ya ce, ya yanke shawarar kaddadar da binciken game da zanga-zangar da aka yi a gaban ofishin majalissar dake garin Gao na arewacin Mali wanda ya yi sanadiyyar a kalla mutuwar uku daga cikin masu boren.
A ranar Talata ne dai mutane suka taru a wajen cibiyar ofishin majalissar na MINUSMA domin nuna kin amincewa da yarjejeniyar da ofishin ta shiga tare da kungiyar ci gaban 'yan tawayen Azawad wadanda suka bukaci kafa nasu yankin na tsaro a wuraren Tabankort, inda 'yan adawa masu dauke da makamai ke ta gwabza fada.
Mutane 3 sun mutu a sanadiyyar hakan, sannan wadansu kusan 7 sun jikkata lokacin da dubban jama'a da suke zanga-zanga suka nemi afkawa cikin sansanin ofishin na MDD a Gao.
Magatakardar na MDD, ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric game da hakan, ya yanke shawarar kaddamar da bincike domin gano salsalan wannan al'amari, yana mai tabbatar wa gwamnatin Mali da dukkan masu ruwa da tsaki cikin wannan lamari game da aniyarsa.
Sannan kuma ya tunatar da dukkan wadanda ke da alhakin wannan lamari da bukatar mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta domin a samu komawa teburin shawarwari cikin sauri a birnin Algiers na kasar Algeriya. (Fatimah)