Kwamitin tsaron MDD ya nuna matukar damuwa don gane da yawaitar tashe-tsahen hankula a kasar Libya, yana mai kira ga daukacin sassan da abin ya shafa, da su mai da hankali kan hanyoyin kawo karshen rigingimun ta hanyar siyasa.
Wakilan kwamitin wadanda suka bayyana hakan ta cikin wata sanarwa, sun kuma yi Allah wadai da yadda rikicin baya bayan nan ya haddasa lalata kayayyaki da gine-ginen hukuma, da keta hakkokin bil'adama, lamarin da sanarwar ta ce na iya haifar da mummunan sakamako ga tsaron yankin baki daya.
Kaza lika sanarwar ta tabbatar da cewa, amfani da karfin tuwa ba zai taba warware wata matsala ba, don haka ya zama wajibi dukkanin masu ruwa da tsaki su koma teburin shawara, ta yadda za a iya kaiwa ga warware matsalolin tsaro da na siyasar kasar cikin lumana.
Rahotanni dai na cewa, fada ya barke a wasu sassan kasar ta Libya, musamman ma a birnin Tripoli da tsaunukan Nafusa, inda aka yi lugudan wuta da jiragen yaki. Sauran wuraren da aka yi dauki-ba-dadin sun hada da Benghazi da wasu yankunan gabashin kasar masu makwaftaka da shi.
Fadace-fadace dai sun sake dawowa a wadannan yankuna ne, 'yan kwanaki kadan, bayan da MDD ta ayyana kudurin dakatar da bude wuta a birnin Benghazi, matakin da ya baiwa fararen hula damar sararawa, tare da binne gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren da suka gabata. (Saminu)