Za a iyar cimma wata yarjejeniya kan nukiliya idan har aka dage dukkanin takunkumi, in ji wani mai shiga tsakanin kasar Iran Abbas Araqchi a ranar Alhamis.
Matsayinmu shi ne na ganin an janye baki dayan takunkumi, a cewar mista Araqchi, mataimakin ministan harkokin waje kasar Iran a wata hira da Press TV, bayan shawarwari tsakanin wakilan kasar Iran da manyan kasashe shida da suke hada da Ingila, Sin, Faransa, Amurka, Rasha da Jamus a birnin Montreux na kasar Switzerland.
Janye takunkumi shi ne muhimmin mataki na shawarwari, kuma babu wani batun sanya wani takunkumi idan har manyan kasashen duniya suna yi da gaskiya wajen cimma wata yarjejeniya tare da kasar Iran, a cewar mista Araqchi.
Dole ne manyan kasashen duniya su zabi tsakanin kokarin cimma wata yarjejeniya, ko kuma ci gaba da matsa wa Iran lamba ta hanyar kakaba mata takunkumi, in ji wannan jami'i. (Maman Ada)