in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Lesotho ya yi alkawarin sake bude majalisar dokokin kasar
2014-09-05 10:24:05 cri

Firaministan kasar Lesotho Tomas Thabane, ya yi alkawarin sake bude majalisar dokokin kasar a ranar 19 ga watan Satumba, kwanaki biyu bayan dawowarsa kasar daga Afirka ta Kudu sakamakon wani juyin mulkin soja.

Wata majiya daga Maseru, babban birnin kasar, ta bayyana cewa, an shirya wata ganawa ranar Jumma'a tsakanin sassan da ke fada da juna, don tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma bisa tsakanin kungiyar SADC.

A karkashin yarjejeniyar, an amince da kafa gwamnatin hadaka wadda kuma za ta baiwa Thabane damar dawowa gida don ci gaba da aikinsa, musamman sake bude majalisar dokokin kasar.

A watan Yuni ne dai Thabane ya rusa majalisar dokokin kasar don guje wa kuri'ar yanke kauna da 'yan majalisar za su kada a kansa, sannan ya tsaya kai da fata cewa, ba za a canza shawarar da ya yanke ta korar kwamandan sojojin kasar Tlali Kamoli ba, matakin da ya harzuka sojojin a karshen makon da ya gabata na yunkurin kifar da gwamnatin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China