in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta bukaci sojojin Lesotho da su koma bariki
2014-09-01 10:18:54 cri

Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta bukaci sojojin kasar Lesotho da su koma barikokinsu, tare da baiwa zababbiyar gwamnatin kasar damar gudanar da harkokin mulki kamar yadda doka ta tanada.

Wannan kira dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da sashen lura da huldodin kasa da kasa, da hadin gwiwa na Afirka ta Kudun ya fitar a karshen mako.

Sanarwar ta kuma tabbatar da mamayar da sojojin kasar ta Lesotho suka yiwa wasu muhimman wurare, tare da sanya takunkumi ga kafofin rediyo da talabijin a kasar. Game da hakan sanarwar ta ce, Afirka ta Kudu na goyon bayan kungiyar AU wajen watsi da haramtaccen juyin mulkin sojin a Lesothon, lamarin da a cewar ta ko alama ba za a lamunta ba.

Bugu da kari sanarwar ta bukaci daukacin masu ruwa da tsaki, musamman ma jagororin gwamnatin hadakar kasar ta Lesotho, da su tabbatar goyon bayansu ga aiwatar da yarjejeniyar Namibia, wadda aka cimma yayin taron kungiyar SADC da ya gudana a 'yan kwanakin baya a kasar Zimbabwe.

Duk dai da zargin juyin mulki da sassa da dama suka yiwa sojojin kasar ta Lesotho, a hannu guda dakarun sojin sun ce, ba juyin mulki suka gudanar ba. A cewar jagororin rundunar, sun dauki matakai ne kawai na dakile keta tsaron kasar da rundunar 'yan sanda ta yi niyar aiwatarwa, tuni kuma suka koma barikokin su kamar yadda doka ta tanada. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China