Wata yarjejeniya da aka rattatabawa hannu tsakanin kasar Sin da kasar Zimbabwe, wacce ta baiwa masu dauke da fasfo na diplomasiyya damar shiga kasashen juna, ba tare da amfani da takardar iznin tafiya ta visa ba, ta fara aiki a watan Nawumba.
Wata majiya ta ofishin ma'aikatar harkokin waje ta Zimbabwe ta ce, yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu tsakanin Zimbabwe da Sin a ranar 25 ga watan Agustan da ta wuce ta fara aiki ne a ranar 12 ga watan Nawumba na wannan shekarar.
Ministan harkokin waje na Zimbabwe Simbarashe mumbengegwi shi ne ya rattaba hannu a kan yarjejeniya a madadain shugaban kasa Robert Mugabe a yayin da ya kawo wata ziyara a kasar Sin a karkashin jagorancin shugaban kasar Robert Mugabe.
Wannan soke amfani da takardar izni na visa ga wadanda ke dauke da fasfo na diplomasiyya ya zo a daidai lokacin da ma'aikatar yawon bude ido ta Zimbabwe take kokarin ganin an ba Sinawa damar samun visa a yayin da suka shiga kasar Zimbabwe domin bunkasa yawon bude ido daga kasar ta Sin, wacce ke yankin Asiya. (Suwaiba)