Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kwato garuruwa 10 da a baya ke karkashin ikon mayakan kungiyar Boko Haram.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaban ofishin tattara bayanai a Najeriya Mike Omeri, ya ce, a jihar Adamawa, garuruwan da sojojin suka karbe sun hada da Hong, da Mubi ta Arewa, da Mubi ta Kudu, da Michika, da Shuwa, da Wuro Gyambi, da Gombi, da Vimtim, da Uba da kuma Bazza.
Sai dai a cewar Omeri, kawo yanzu garuruwan Madagali, da Gulak, da Wagga-Mildo, da Shelini/Vapra, da Sabon-Gari da Gubla na hannun mayakan kungiyar.
A jihar Yobe kuwa garuruwan da sojojin suka kwace sun hada da Gujba, da Gulani.
Har wa yau Mr. Omeri ya zayyana garuruwan Mafa, da Gamboru-Ngala, da Mallam Fatori, da Abadam, da Marte da ke jihar Borno, cikin jerin garuruwan da sojojin kasar suka kwace bayan sun fatattaki mayakan na Boko Haram.
Daga nan sai shugaban ofishin tattara bayanan na Najeriyar ya jinjinawa kwazon dakarun sojin kasar, bisa namijin aikin da suke gudanarwa, ciki hadda kare birnin Maiduguri, daga yunkurin da mayakan Boko Haram suka yi na karbe birnin. (Saminu)