in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta amince da tawagar share fagen babban zabe zuwa Sudan
2015-03-04 10:58:10 cri

Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta amince da a tura tawagar share fagen babban zaben dake tafe a kasar Sudan da za'a yi a ranar 13 ga watan Afrilu, kamar yadda sanarwa daga kungiyar ta nuna.

Makasudin aikin tawagar shi ne su yi nazarin halin shirin da aka yi ya zuwa wannan lokacin domin babban zaben daga dukkan masu ruwa da tsaki, sannan kuma su duba yadda aka shirya yin zaben domin tabbatar da an gudanar da shi bisa yarjejeniyar aiwatar da demokradiya, zabe, mulki na Afrika wanda Sudan na daga cikin wadanda suka rattaba hannu, in ji sanarwar.

Makasudin hakan kuwa ya hada da nazarin karfin da bukatar babbar hukumar zabe don samar da irin taimakon da ta ga ya dace da kungiyar ta AU ta bayar, sannan kuma ta ba da shawarwarin da suka shafi yanayi da aikin tawagar sa ido a zaben.

Tawagar share fagen zaben ta kunshi jami'i a sashin harkokin siyasa wanda zai zama mai jagoranta, sai kuma masana kan zaben masu zaman kansu guda 4.

A lokacin aikin tawagar, ana sa ran za ta tattauna da masu ruwa da tsaki a bangaren siyasar kasar ta Sudan tun daga ranar 1 zuwa 10 ga watan da muke ciki na Maris, kamar yadda sanarwar ta yi bayani. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China