Shugaban kasar Sudan Omar al-Bsshir ya ba da tabbatanci a ranar Lahadi wajen cimma zaman lafiya a cikin kasar a shekarar 2015 ta hanyar shawarwari ko ta karfin soja.
Shekarar da muke ciki za ta kasance shekara ta samun zaman lafiya a dukkan yankunan kasar ta hanyar shawarwari, ko ta hanyar yaki, in ji shugaba al-Bashir a yayin da yake jawabi a gaban miliyoyin magoya bayansa a Kagogle, babban birnin jihar Kudancin Kordofan, dake fama da yaki tsakanin sojojin gwamnati da mayakan kungiyar kwato 'yancin al'ummar Sudan ta arewa (SPLM-N).
Shugaba al-Bashir, 'dan takarar jam'iyyar NCP mai mulki, na wani rangadi a biranen kasar Sudan bisa tsarin yakin neman zabe domin zabukan shugaban kasa, da na 'yan masalisa.
Haka kuma ya jaddada niyyarsa cewa, gwamnati na tattauanawa da yin shawarwari domin samar da zaman lafiya, inda kuma ya kara da cewa, ba za mu rufe kofa ba kafin yin shawarwari tare da 'yan tawaye, domin samun zaman lafiya ta hanyar shawarwari na taimakawa wajen kaucewa zubar da jinin al'ummar Sudan.
An dai bude yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a ranar Talata tare da halartar jam'iyyun siyasa 44, da kuma 'yan takara 16 a zaben shugaban kasar. (Maman Ada)