Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya ce, zai yi murabus har al'ummar kasar ta bukaci hakan, ta kin sake zaben shi a babban zaben dake tafe.
Al-Bashir, 'dan takara a jam'iyyar dake mulkin kasar National Congress Party NCP, a ranar Alhamis din nan ya kaddamar da yakin neman zaben shi daga Medani a jihar Gezira, inda yake neman sake darewa karagar mulkin kasar a karo na uku.
Dubban magoya bayan shugaban da jam'iyyar sun taru a dandalin birnin Medani dauke da alluna da kyallewa dake nuna goyon bayansu ga shugaban kasar al-Bashir.
Shi dai shugaba al-Bashir ya sake nanata kiran shi ga tattaunawa ta kasa, a inda ya ce, har yanzu suna kira ga 'yan adawa da masu dauke da makamai da su kawo bukatunsu a kan teburin shawarwari su kuma mutunta ra'ayin masu rinjaye, domin wannan shi ne demokradiya. (Fatimah)