in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane sama da dubu 40 ne suka rasa gidajensu a arewa maso yammacin Najeriya a 2014
2015-01-23 10:14:35 cri

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, jimillar mutane 44,398 ne suka rasa matsugunansu a sassan arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 2014.

Jami'in shiyya na hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya (NEMA) Musa Ilallah wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce, wadannan mutane sun rasa gidajen nasu ne sakamakon fadan kalibanci da hare-haren masu tada kayar baya, galibin su daga jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, da kuma jihohin Jigawa da Kano da Kaduna da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Ilallah ya ce, kimanin bama-bamai 13 aka tayar a wannan yankin a shekarar da ta gabata, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 248, kana 435 suka jikkata, baya ga wasu bama-bamai 11 da aka tayar a birnin Kano, kana wasu guda biyu suka fashe a garin Kaduna.

Jami'in na NEMA ya ce, mutane 945 ne bama-babai da fadan kalibanci da hare-haren masu tada kayar baya suka hallaka a shekarar da ta gabata a jihohin guda uku. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China