in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole gwamnatin Somalia ta dauki matakin yakar 'yan fashin teku, in ji babban jami'in MDD
2014-10-23 14:28:01 cri

Karamin sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa, Jeffrey Feltman ya ce, idan har ana so a magance matsalar fashin jiragen ruwa a gabar ruwan Somalia, dole ne sai gwamnati da hukumomin cikin kasa, sun dauki mataki na samawa jama'a wasu hanyoyin samun abinci.

Karamin sakataren ya yi wannan jawabin ne a yayin da yake jawabi ga kwamitin tsaro na MDD a game da maganar fashin da ake yiwa jiragen ruwa a kusa da gabar ruwan kasar Somalia.

Feltman ya ce, daukar mataki na samar da ayyukan yi zai taimaka wa Somalia ta magance matsara fashin jiragen ruwa.

Raguwar kai hare-hare daga bangaren barayi a gabar ruwan Somalia wata dama ce da aka samu domin binciken kokarin da ake gudanarwa a yanzu da kuma daukar matakai da za su dakile fashin jiragen ruwa ta hanyar samar da ayyukan yi, tare kuma da magance matsaloli na tashin hankali na siyasa da rashin ayyukan yi.

Karamin sakataren MDD ya ce, dole ne 'yan kasar Somalia su gina kasarsu tare da bai wa jama'a damar taka rawa a mulkin kasar.

Feltman ya kara da cewar, dole ne kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Somalia, a bisa kokarin da take yi na daukar nauyin da ke wuyanta, kamar yadda aka tsara wata yarjejeniyar ci gaba ta shekara ta 2016.

Feltman ya kuma ce, ya zama tilas MDD ta dauki mataki na siyasa domin taimakawa Somalia da sauran kasashe dake yankin daukar matakai na shari'a a kan masu fashin jiragen ruwa dake yankin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China