in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da daukan matakan da za su kare kananan yara daga yaki
2013-09-11 10:16:31 cri

Wata babbar jami'a a MDD ta ce, akwai bukatar daukan matakan da suka dace domin kare miliyoyin yara kanana a duniya daga masifun da suka shafi yaki.

Leila Zerrougui, wakiliya ta musamman ta MDD a kan yara da al'amurran da suka shafi tashin hankali da makamai ta shaida ma taron majalissar na 24 a kan 'yancin dan adam cewa, yara kanana ne suka fi shan wahala a duk inda ake yaki ko tashin hankali.

Da take ba da misali da kasar Syria, Leila Zerrougui ta ce, tun lokacin da aka fara tashin hankali, yara miliyan uku ne suka yi gudun hijira ko suka rasa muhallinsu cikin kasar, inda sakamakon rufe makarantu, kuma kusan yara miliyan biyu ne suka daina zuwa makarantar.

Ta yi bayanin cewa, a duk inda ake fuskantar tashin hankali, an samu karuwan mummunan sakamako a kan yara idan aka cire 'yancinsu na samun ilimi, ana kashe su ko a nakasa su ko kuma su fada hannun bata gari a ci zarafinsu, sannan kuma jami'an tsaro na soji da ma na adawa na amfani da su wajen ba su makamai, ko kuma ma a kama su a tsare tare da gana masu azaba don kawai ana zargin suna da alaka da wassu jam'iyyu ko kungiyar adawa.

Daga nan sai madam Leila Zerrougui cikin bayaninta ta yi kira da a kara ba yara fifiko ga batutuwa da suka shafi tattalin arziki, walwala da al'adunsu a lokacin kare su daga tashin hankali, sannan kuma a yi kokari na hadin gwiwwa domin gano hanyoyin da za'a tabbatar da cewa, yaran sun samu ilimi, da kula da kiwon lafiyarsu yadda ya dace bisa bukata da yanayin da suke ciki lokacin yaki ko idan suka rasa muhallansu sakamakon hakan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China