Bayan kammala babban taron jam'iyyar na kwanaki biyu, jam'iyyar adawa ta ANC ta tsai da a ranar Asabar 'dan takararta Jean-Pierre Fabre a matsayin 'dan takara a zaben shugaban kasar Togo da aka tsai da shiryawa a farkon watannin uku na shekarar 2015.
Mista Fabre ya yi fice sosai a tsawon shekaru da dama a fagen siyarar kasar Togo domin kasancewarsa a tsawon shekaru a matsayin sakatare janar na jam'iyyar adawa ta UFC da ta aza shi a matsayin 'dan takara a zaben shugaban kasa na watan Maris din shekarar 2010. (Maman Ada)