in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Kenya na daukar karin matakan tsaurara tsaro
2015-03-03 09:54:57 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta ce, tana daukar karin matakan tsaurara tsaro a dukkanin sassan kasar, bayan da ta samu rahotanni dake cewa, kungiyar Al-shabaab na shirin kaddamar da hare-hare a kasar.

Mukaddashin babban sifeton 'yan sandan kasar Samuel Arachi ne ya tabbatar da hakan ga majiyarmu, yana mai cewa, rahotannin sirri sun nuna aniyar kungiyar na kaiwa majalissar dokokin Kenyan farmaki.

An ce, wasu maharan kungiyar su 12 ne ke shirin kaddamar da harin, kuma mai yiwuwa ne cikin su tuni 6 sun shiga Kenyan daga kasar Somaliya.

Hakan dai na zuwa ne bayan da kasar Masar ta bukaci mahukuntan Kenyan da su samar da karin tsaro ga ofishin jakadancinta dake kasar, da ma sauran gine-ginen kasar ta Masar dake Kenyan.

Wata jaridar Kenya ta ce, bayanan da ta tattara sun nuna cewa, wani mai suna Mohammed Mohamud ne ake zargin zai jagoranci kaddamar da harin, wanda kungiyar ta Al- Shabaab mai alaka da Al-Qaida ta shirya.

Rundunar 'yan sandan na Kenya dai ta ce, za ta tabbatar da kare dukkanin gine-ginen hukuma a dukkanin sassan kasar, da ma duk wani wuri da ake zaton mayakan Al-Shabaab din na iya kaiwa farmaki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China