in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta samar wa jami'an tsaro tsarin sa ido na dala miliyan 141
2014-05-15 10:34:19 cri

Gwamnatin kasar Kenya za ta kashe dalar Amurka miliyan 141 sayen wani tsarin sadarwa da sanya ido domin taimakawa jami'an tsaron kasar wajen karfafa tsaro a cikin wannan kasa dake gabashin nahiyar Afrika.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, kamfanin Safaricom, za'a baiwa nauyin aiwatar da wannan tsarin sanya ido da sadarwa na tsaron jama'a, kuma za'a kammala shi a cikin watanni hudu masu zuwa.

Ina son a kammala shi cikin gaggawa, domin wannan tsari na da muhimmanci ga tsaron kasarmu, in ji mista Kenyatta, tare da bayyana cewa, fatansa shi ne, na ganin wannan aiki ya tabbata cikin gajeren lokaci. Wannan tsarin sanya ido zai hada duk wasu cibiyoyin dake kula da harkokin tsaro, ta yadda za'a tattara bayanai cikin hadin gwiwa da hedkwatar dake kula da ayyukan tsaro. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China