in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a dauki sabbin jami'an 'yan sanda a Kenya
2014-04-14 09:47:10 cri

Mahukunta a Kenya sun bayyana shirin daukar karin jami'an 'yan sanda kimanin 10,000 aiki, domin bunkasa ayyukan tsaron kasar.

Mataimakin shugaban kasar ta Kenya William Ruto wanda ya tabbatar da hakan a jiya Lahadi, ya kuma ce, gwamnatin kasar mai ci, ta yanke shawarar daukar sabbin jami'an 'yan sandan ne a matsayin wata hanya, ta tallafawa yakin da ake yi da ta'addanci, da ma sauran miyagun laifuka.

Ruto ya kara da cewa, mahukuntan kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba, wajen daukar dukkanin matakan da suka dace, wajen dakile ayyukan ta'addanci, don haka ne ma, a cewarsa, za a kara yawan kudaden da ake kashewa wajen samar da kayan aiki na zamani, da ba da horo ga jami'an tsaron kasar.

Daga nan sai mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa, Kenya ba ta da niyyar tattaunawa da 'yan ta'adda, ko masu goya musu baya, har sai an kai ga kawar da barazanar su a dukkanin fadin kasar, da ma yankin na gabashin Afirka baki daya.

Tuni dai mahukuntan kasar Kenyan suka nuna damuwa don gane da karuwar hare-haren ta'addanci dake aukuwa a sassan kasar, matakin da ke disashe martabar kasar, tare da gurgunta fannin yawon shakawa da kasar ke tinkaho da shi. Lamarin da ya janyo kiraye-kirayen gano musabbabin hakan, da kuma bukatar daukar matakan shawo kan matsalar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China