in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaurara matakan tsaro a gundumar Lamun Kenya
2014-07-14 09:30:21 cri

Jami'an tsaron kasar Kenya sun tsaurara matakan tsaro a gundumar Lamu, bayan da wasu dakaru dauke da makamai suka kaiwa kauyen Pandanguo farmaki a daren ranar Asabar.

A cewar rundunar 'yan sanda, bata garin sun kone gidaje, da wata makaranta, tare da lalata wani asibitin shan magani, kafin su wawashe kayan amfanin gona da aka adana a wani dadin ajiya, a wata gona dake dajin Boni, mai makwaftaka da teku.

Har ila yau rundunar 'yan sandan ta ce, wasu rukunin maharan, sun yi garkuwa da wata babbar mota, dake makare da kayan abinci a yankin Hindi, suka kuma sace kayan da take dauke da su.

Da yake karin haske game da aukuwar lamarin, kwamishinan gundumar ta Lamu Miiri Njenga, ya ce, a watan Yunin da ya gabata ma dai irin wannan hari ya janyo asarar rayukan mutane 60, tare da raba daruruwan fararen hula da gidajen su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China