A dunkule kashi 21,5 cikin 100 na al'ummar kasar Afrika ta Kudu sun yi rayuwa cikin kangin talauci a shekarar 2014, a cewar wasu alkaluman da aka fitar a ranar Talata. Wannan shi ne wata karuwa ta kashi 1,5 cikin 100 idan aka kwatanta da alkaluman shekarar 2010, a yayin da kashi 20 cikin 100 na al'ummar kasar Afrika ta Kudu ke rayuwa cikin kangin talauci, in ji wani rahoton hukumar kididdiga ta kasar Afrika ta Kudu wato Statistics South Africa.
Babban masanin kididdiga, Pali Lehohla ya jaddada a cikin rahoton cewa, a yayin da mizalin taulaci ya karu, tsadar rayuwa karuwa take. A shekarar 2014, ana bukatar da rands 355 kimanin dalar Amurka 31, ga matsakaicin 'dan Afrika ta Kudu domin sayen abinci ko wane wata, abin da ya karu da rands 34 idan aka kwatanta da na shekarar 2010. (Maman Ada)