in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin babbar aminiyar Mali ce, in ji uwargidan shugaban kasar
2015-02-13 11:51:12 cri

Uwargidan shugaban kasar Mali Keita Aminata Maiga ta bayyana cewa, kasar Sin babbar aminiyar Mali ce ne a yayin da take jawabi a wurin wata liyafa wadda jakadan kasar Sin a Mali Lu Huiying ya shirya domin kara dankon zumunta tsakanin kasashen biyu a Bamako a daren Talatar da ta gabata.

Madam Aminata ta ce, abokantakar tsakanin kasarta da Sin ta samo asali tun wajen shekarun 1960, wannan dadewa dangantaka na daya daga cikin dalilin da ya sa ta halarci liyafar da jakadan Sin ya shirya.

Uwargidan shugaban kasar Mali ta ce, kawo ya zuwa yanzu kasar Sin ta yiwa kasar Mali abubuwa da dama kuma ta yi amanna kasar Sin za ta ci gaba da yiwa Mali ayyuka da dama domin taimakawa bukatun kasar.

A nashi jawabin, jakadan kasar Sin a Mali Lu Huiying ya ce, dankon zumunci ya kara kulluwa tsakanin kasashen biyu, tun shekarar 2014, bayan da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya kawo ziyara kasar Sin.

Lu ya ce, an kwashe shekaru 55 ana hulda tsakanin Mali da Sin saboda haka ya bukaci kasashen biyu da su yi amfani da wannan dama domin kaiwa ga wani matsayi na kara dankon dangantakar kasashen 2. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China