in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mayakan Boko Haram 500 a arewacin Najeriya
2015-02-03 09:27:54 cri

Hedkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa, dakarunta sun kashe mayakan Boko Haram a kalla guda 500 a garin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar.

Cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, hedkwatar tsaron Najeriyar ta ce, sojojin nata sun samu wannan nasara ce, yayin da mayakan na Boko Haram ke kokarin kaddamar da wani hari da sanyin safiyar ranar Lahadi a garin na Maiguduri.

Wani jami'in tsaro ya shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, sama da mayakan Boko Haram 500 ne aka hallaka yayin wannan bata kashi. Ko da yake ya zuwa yanzu al'amura sun lafa a wuraren da aka yi dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu dai an kafa shingayen duba ababan hawa da dama don tabbatar zaman lafiya da tsaro a garin na Maiduguri. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China