in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Chadi sun bayyana damuwa kan tashin hanhali a nahiyar
2015-01-29 10:04:22 cri

Kasashen Sudan da Chadi a ranar Laraban nan suka bayyana damuwarsu game da yawan tashe-tashen hankula dake wanzuwa a Libya, Sudan ta Kudu, jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Nigeriya da kuma wanda yake faruwa a yankin Darfur na kasar ta Sudan.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na Chadi Idriss Deby suka ambata wannan damuwa a tattaunawarsu a birnin Khartoum.

Shugaba Bashir ya sanar wa manema labarai bayan tattaunawar tasu cewa, gaba daya nahiyar tana fuskantar barazanar tsaro da ta shafi kasashen na Sudan da Chadi. Daga nan sai ya bayyana godiyarsa bisa ga kokarin da kasar ta Chadi ta yi na ganin an samu zaman lafiya a yankin Darfur da kuma kokarin shugaba Idriss Deby na taka rawar gani wajen tabbatar da warware rikicin.

A nashi bangaren, shugaba Idriss Deby ya jaddada aniyar kasarsa na ganin ta samar da zaman lafiya a yankin Darfur dake fuskantar fada da makamai, yana mai jadadda cewar, tattaunawa kadai hanyar da ta dace wajen kawo karshen rikicin na Darfur da kawo karshen wahalar da al'ummar wajen ke fuskanta.

Idriss Deby ya isa birnin Khartoum ne na kasar Sudan a ranar Laraba domin fara ziyarar aiki ta yini biyu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China