Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu da watannin 6. Don haka bisa sabon wa'adin, yanzu tawagar ta UNMISS za ta kammala aikinta ne a ranar 30 ga watan Mayun shekara mai zuwa.
Kwamitin wanda ya cimma wannan matsaya a zamansa na jiya Talata, ya kuma bukaci mahukuntan Sudan ta Kudu, da sauran masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe wajen cimma nasarar ayyukan tawagar ta UNMISS, musamman ma a fannin ba da kariya, da tsaro, tare da baiwa jami'an ta damar shiga dukkanin sassan kasar domin gudanar da ayyuka.
Kaza lika kwamitin ya zayyana muhimman ayyukan tawagar, ciki hadda baiwa fararen hula kariya, da sa ido tare da gudanar da bincike game da batutuwan da suka jibanci kare hakkokin bil'adama.
Sauran sun hada da taimakawa aikin shigar da kayayyakin jin kai, da kuma aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin sassan da rikicin kasar ya shafa.
Har wa yau an bukaci daukacin sassan da ba sa ga maciji da juna, da su kai zuciya nesa, tare da tabbatar da kare hakkokin bil'adama, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. (Saminu)