in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi tir da korar jami'an MDD daga Sudan
2014-12-26 15:28:58 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi tir da matakin da gwamnatin Sudan ta dauka na korar jami'an MDD daga kasar.

Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ta bayyana daukar wannan mataki kan jami'an MDDr su 2, dake aikin bisa dokokin kasa da kasa, a matsayin wani mataki da ba za a amince da shi ba. Mr. Ban ya kuma yi kara ga mahukuntan Sudan din da su sake shawara kan wannan mataki, su kuma hada kai da MDDr domin cimma nasarar da aka sanya gaba.

Rahotanni dai sun tabbatar da korar Ali Al-Za'tari, wanda ke matsayin babban jami'in tsare-tsare na MDD a Sudan, da kuma Yvonne Helle, daraktan hukumar UNDP a kasar.

Hakan kuma na zuwa ne 'yan kwanaki kadan, bayan da mahukuntan kasar suka hana wasu ma'aikatan wanzar da zaman lafiya damar shiga wani yanki dake yammacin Darfur, yankin da ke fama da yawan tashe-tashen hankula, ake kuma zargin an yiwa mata kimanin 200 fyade. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China