in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya jaddada kin amincewa ga 'yancin mulki kan kudancin Kordofan da Blue Nile
2014-12-01 10:50:55 cri

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya jaddada kin amincewarsa ga cikakken 'yancin mulkin kai ga kudancin Kordofan da Blue Nile, wadanda ke fuskantar tashe tashen hankali tsakanin sojojin kasar da 'yan tawaye na Sudan People's Liberation Movement SPLM reshen arewaci.

Shugaba al-Bashir ya ce, ba za'a amince da duk wata yarjejeniyar da za ta ba da dama ga wadannan wurare biyu su samu 'yancin mulkin kansa da kansu ba. Tun da farko dai tawagar kungiyar 'yan tawayen ta SPLM reshen arewacin kasar a tattaunawar su wajen cimma yarjejeniya a birnin Addis Ababa na kasar Habasha sun bukaci a ba su 'yancin mulkin kansu cikin daya daga bukatunsu idan har ana son samar da zaman lafiya cikin tsarin dokokin Sudan mai kabilu daban daban, kuma karkashin demokradiya.

Shugaban ya kara da cewa, idan har aka ce haka to sai dai sauran yankuna kamar gabashin Sudan, Darfur da Gezira a tsakiyar kasar ta Sudan su ma a ba su 'yancin mulkin kansu da kansu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China