in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya kara wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya dake Abyei
2013-11-26 09:59:59 cri

Kwamitin tsaron MDD ya amince da kara wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNISFA a yankin Abyei, yankin da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kansa.

Wani kuduri da ya samu amincewar mambobin kwamitin 15, ya baiwa tawagar karin watanni 6, tare da kira da a kara yawan dakaru dake aikin na tabbatar da zaman lafiya a wannan yankin.

Bisa amincewar da aka yi da wannan kuduri, yanzu haka tawagar ta UNISFA za ta ci gaba da kasancewa a yankin na Abyei, har ya zuwa ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2014 dake tafe. Ana kuma fatan kara yawan rundunar zuwa 5,326.

Daukar matakin kara yawan dakarun dai na da nasaba da burin da ake da shi, na karfafa tsarin tsaron kan iyakokin kasashen biyu, wanda ke kunshe cikin jarjejeniyar da sassan biyu suka amincewa, don gane da samun 'yancin Sudan ta Kudu a shekarar 2011 da ta shude. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China