in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a manta da 'yan matan Chibok ba, in ji Ban Ki-moon
2014-07-24 09:43:26 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana goyon bayansa ga gangamin da al'ummun duniya ke yi, domin jimamin cika kwanaki 100, da sace 'yan matan nan na Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi a Najeriya.

Mr. Ban wanda ya ce, ko alama duniya ba za ta taba mantawa da lamarin 'yan matan ba, ya kuma jaddada kira game da gaggauta sakin yaran ba tare da wani bata lokaci ba.

Babban magatakardar MDDr ya kuma yi kira ga gamayyar kasashen duniya, da su ci gaba da hadin gwiwa wajen marawa yunkurin da ake yi na kubutar da 'yan matan baya.

A jiya Laraba ne dai kungiyoyi da dama a sassan duniya daban daban, suka gudanar da tarukan nuna jimami, domin nuna takaici ga tsawaitar lokacin da 'yan matan suka yi a tsare, duka dai da nufin janyo hankalin duniya ga munin wannan lamari.

Tun dai ran 14 ga watan Afirilun da ya gabata ne dai kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan su 270, daga makarantarsu dake garin Chibok a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, ta kuma yi barazanar sai da su. Kuma kawo yanzu, duk wani yunkuri da kwararru na kasa da kasa suka yi domin ceton 'yan matan ya ci tura. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China