Majalissar dokokin kasar Libya karkashin jam'iyyar GNC ta bakin wakilinta a ranar Talatar nan ta bayyana cewa, tattaunawar sulhu tsakanin ta da jam'iyyar adawa da MDD ke shiga tsakani, an dakatar da ita sai yadda hali ya yi.
Wakilin jam'iyyar ta GNC a Tripoli Mohammed Amazb ya ce, manzon MDD a Libya Bernardino Leon ya sanar da ita cewa, an dage tattaunawar da za'a yi a ranar Alhamis din nan a Morocco har sai yadda hali ya yi.
Shawarar hakan ta zo ne kwana daya bayan da majalissar wakilan kasar da duniya ta amince da ita a Libyan wadda take zama a garin Tobruk ta yanke shawarar ficewa daga cikin tattaunawar, tare da zargin cewa, jam'iyyar GNC tana yada tashe tashen hankali, ta'addanci da kuma tsattsauran ra'ayi.
Libya dai tana fuskantar rigingimun siyasa tun shekarar 2011 bayan da aka hambarar da gwamnatin marigayi shugaba Muammar Gaddafi, yanzu kuma tana ta fama ne tsakanin majalissar dokoki guda biyu da gwamnatoci biyu, kowace na adawa da dan uwanta. (Fatimah)