Bangarori masu gaba da juna a kasar Libiya sun sake komawa kan teburin shawarwari a karkashin jagorancin MDD a birnin Ghadames dake kudu maso yammacin kasar, bisa wani kokarin warware rikicin da kasar ke fuskanta a halin yanzu tsakanin bangarori dake gaba da juna da ko wane ke da gwamnatinsa da kuma majalisar dokokinsa.
Dukkan bangarorin sun isa birnin na Ghadames, har ma da 'yan majalisun dokokin babban taron kasa na CGN, a cewar wani wakili na tawagar zaman lafiya ta MDD ta kasar Libiya, tare da kara bayyana cewa, ana ci gaba da wasu shawarwarin na daban, da masu ruwa da tsaki a fagen siyasa da kungiyoyin daba daban na Libiya za su shiga, wadanda kuma za su gudana tare a Geneva. (Maman Ada)