Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya NEMA, ta ce, a kalla mutane 3,200 ne suka kauracewa gidajen su, sakamakon harin baya bayan nan da 'yan Boko Haram suka kaddamar a garin Baga dake jihar Borno.
A cewar kakakin hukumar Manzo Ezekiel, an tura jami'an NEMA zuwa yankunan da 'yan gudun hijirar ke samun mafaka domin tallafa masu.
Ezekiel ya ce, da dama daga 'yan gudun hijirar na samun mafaka ne a birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar ta Borno, inda NEMAn da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke ba su tallafin jin kai da ya dace.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 3 ga watan Janairun nan ne mayakan kungiyar Boko Haram suka yi dirar mikiya kan garin na Baga, inda suka samu nasarar kwace sansanin sojoji dake garin, lamarin da ya tilasawa dubban al'ummar garin tserewa.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a kalla mutane 135,000 ne suka fice daga yankin arewa maso gabashin Najeriya zuwa makwaftan kasashe, yayin da wasu kimanin 850, 000 ke samun mafaka a cikin kasar. (Saminu)