Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar a ranar Talata na nuna cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna da takwaransa na kasar Angola Georges Rebelo Chikoti a nan birnin Beijing, don bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Sanarwar ta ruwaito Wang Yi na cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Angola a bangaren aikin gona, makamashi, kayayyakin more rayuwa da sauransu, ta haifar da kyakkyawan sakamako, kuma kasashen biyu na amfana da dankon zumuncin da ke tsakaninsu.
Kasar Sin na son hada kai da kasar Angola don bunkasa dangantakatar da ke tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi tare da kara bayar da gudummawa wajen ci gaban Afirka cikin lumana.
A nasa jawabin, Chikoti ya yaba da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, ya ce, kasar Angola ta yaba da goyon bayan da Sin ta baiwa kasar Angola wajen sake gina kasar bayan yaki, kuma a shirye take ta kara fadada hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin sassan biyu. (Ibrahim)