in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana na fatan shigar da Delta Okavango cikin jerin kayayyakin tarihin duniya
2014-06-18 10:39:48 cri

Kasar Botswana ta bayyana imaninta cewa, yankin Delta Okavango da ya yi fice a matsayin wata mattarar ruwan kasar na shirin shiga cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya a yayin taro na 38 na kwamitin kayayyakin tarihin duniya na UNESCO da zai gudana a Doha na kasar Qatar, in ji Game Gareanna, jami'in sadarwa a ofishin ministan yawon bude na kasar. Yankin ruwan Delta Okavango na arewacin kasar Botswana, na daya daga cikin manyan yankunan ruwan Delta dake tsakiyar kasa a duniya. Kuma yanki ne da ake samun a cikin yanayin damuna ko na rani mai yawan nau'o'in halittu, da kuma ke janyo hankalin masu yawon bude ido. An fara kamfen neman shigar da Delta Okavanga a cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya yau da kusan shekaru biyu, kuma wannan fitaccen wuri zai samu gajiyar yawon bude ido da tattalin arziki bisa wannan mataki idan haka ya tabbata.

Botswana na fatan samun nasara wajen ganin an sanya Delta Okavango cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya a wannan karo, in ji mista Gareanna.

A cewar ofishin ministan yawon bude idon kasar, zaben na Botswana zai kasance bisa sharudan wannan kasa game da yarjejeniyar kula da kayayyakin tarihi na duniya. Kuma mambobin 21 na kwamiti ne za su gudanar da wannan zaben a yayin zaman taron na Doha. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China