Kwanaki biyu bayan nadinsa, faraministan kasar Mali Modibo Keita ya kafa sabuwar gwmnatinsa, a cewar gidan rediyon kasar a ranar Asabar da yamma. Sabuwar gwamnatin na kunshe da mambobi 29, maimakon 33 dake cikin tsohuwar gwamnatin. Haka kuma sabuwar gwamnatin ta dan bambanta da tsohuwar, tare da shigowar sabbin ministoci shida, da suka hada da 'yan takara biyun da suka kaye a zaben shugaban kasar na watan Yulin shekarar 2013, wato Dramane Dembele na jam'iyyar Adema da aka nada ministan tsara birane da gidaje, sai kuma Choguel Kokalla Maiga na jam'iyyar MPR wanda ake nada ministan sadarwa. (Maman Ada)