Mambobin majalissar ba da shawara a tarayyar Najeriya, sun amince da gudanar da babban zaben kasar dake tafe kamar yadda aka tsara a baya. Sai dai sun amince da yiwuwar dage zaben a yankunan da rikicin Boko Haram ya fi shafa.
Yayin ganawar kusan sa'o'i 8, da mambobin majalissar mai kunshe da tsaffin shuwagabannin kasar, da gwamnati, da kusoshin gwamnati suka gudanar a jiya Alhamis, an tattauna game da kalubalen tsaro dake addabar kasar.
Hankulan duniya dai sun karkakata ga sakamakon wannnan muhimmin taro da ya gudana a fadar gwamnatin Najeriyar, sakamakon zargin da wasu ke yi cewa, wata kila gwamnatin kasar mai ci, na da burin tursasa hukumar zaben kasar ta dage zaben dake tafe.
Da yake karin haske game da matsayar da aka cimma, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya shaida wa 'yan jarida cewa, hukumar gudanar da zaben kasar INEC, ta tabbatar da cewa, za ta kammala raba katunan zabe na din din din ga 'yan kasar, za kuma ta iya gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.
Kaza lika Okorocha ya ce, su ma jagororin hukumomin tsaron kasar sun tabbatar da kammala shirin samar da tsaro yayin babban zaben, ko da yake sun ce, akwai rashin tabbas, game da yanayin da za a iya fuskanta, a yankunan da Boko Haram ke kaka-gida.
Yanzu haka dai za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalissar tarayyar kasar ne a ranar 14 ga watan nan, yayin da zaben gwamnoni da 'yan majalissun jihohi zai biyo baya a ranar 28 ga wata. (Saminu)