in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta hana yawo kan babura a jihar Gombe dalilin kamfen zabuka
2015-02-03 10:38:18 cri

Yan sandan jihar Gombe, dake arewa maso gabashin Najeriya, sun aza wata dokar wucin gadi ta hana zirga zirga kan babura, domin a halin yanzu jam'iyyun siyasa na yakin neman zabe a jihar.

Shugaban Najeriya Goodlock Jonathan na jam'iyyar PDP mai mulki zai shirya kamfenta a ranar Litinin, a yayin da kuma 'dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, janar Muhammadu Buhari mai ritaya zai yi nasa a ranar Talata a jihar.

Matakin na da manufar tabbatar da cewa, 'yan sanda na sanya ido kan zirga zirgar masu babura a cikin jihar Gombe, in ji kakakin 'yan sandan jihar, Fwaje Atajiri a ranar Litinin.

A cewarsa, mutane biyar sun mutu a cikin wasu tagwayen hare hare a ranar Lahadi a wasu wurare daban daban na birnin Gombe.

Fashewar ta farko faru a cikin wata tsohuwar kasuwar Gombe, ta hallaka mutane biyu da ake zargin 'yan kunar bakin wake ne, da jikkata mutum guda, kana harin na biyu, an kai shi ne kan wata kasuwar itace ta Gombe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da jikkata mutane bakwai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China